Postpartum

Lydia postpartum IUD ana sata ne bayan haihuwa ko kuma bayan awa 48 bayan haihuwa, a lokacin mahaifa na bude kunga ba wani zafi sosai a yayin sanya ta. Irin wannan IUD din an yita ne don masu jego , kuma tana taimakawa kwarai don bada tazarar haihuwa ga masu jego kafin suyi arba’in.

Tana rage miki yawan zirga zirgan zuwa asibiti bayan sati 6 don sa IUD ,ko kuma daukan wani cikin nan take bayan haihuwa. Tana bada tazarar haihuwa har na tsawon shekaru 10, amma in ana son haihuwa kafin wannan lokacin za a iya zuwa asibiti don cireta.

This entry was posted on Friday, November 24th, 2017 at 12:54 am and is filed under . You can follow any responses to this entry through the RSS 2.0 feed. Both comments and pings are currently closed.

Comments are closed.

To know more about other pregnancy prevention methods, visit www.honeyandbanana.com